in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarai na Afirka na fatan taron CPC zai bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka
2017-10-25 10:42:53 cri

A yayin da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 19 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kafofin watsa labarai daban-daban na nahiyar Afirka na fatan ganin karin kyakkyawar makoman a akalar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka.

Jaridar Peoples Daily da ake wallafawa a Najeriya ta rubuta wani sharhi dake cewa, kasar Sin ta samu nasarori masu tarin yawa karkashin jagorancin Xi Jinping, wadanda suka yi tasiri ba kawai ga al'ummar Sinawa ba har ga sauran kasashen duniya.

Sharhin jaridar ya kara da cewa, a 'yan shekarun baya-bayan nan kasashen biyu sun amfana da alakar dake tsakaninsu, inda ta ba da misali da kayayyakin more rayuwar jama'a da kasar ta Sin ta gina a wasu kasashen nahiyar, musamman tun bayan taron kolin dandalin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da ya gudana a watan Disamban shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, inda kasar ta Sin ta bayyana kudurinta na taimakawa kasashen Afirka a fannin raya masana'antu da zamanantar da aikin gona, da samar da taimakon kudi na dala biliyan 60.

Ita ma jaridar Leadership da ake wallafawa a tarayyar Najeriya, ta bayyana cewa, Najeriya na daga cikin kasashen Afirka da suka ci gajiyar hadin giwar dake tsakanin kasashen biyu. Ita kuma jaridar Cameroon Tribune na cewa, yanzu haka kasar Sin ce babbar abokiyar nahiyar Afirka a fannonin cinikayya, zuba jari, kana kasar dake kan gaba wajen samar da kudaden gina muhimman kayayyakin rayuwa. Duk da haka alakar dake tsakanin sassan biyu za ta kara bunkasa.

Jaridar ta ce, baya ga kayayyakin more rayuwa da kasar Sin ta samar a galibin kasashen nahiyar biyo bayan wasu yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka kulla, har yanzu kasar Sin tana taimakawa nahiyar wajen gina yankunan masana'antu wadanda za su taimaka wajen rage matsalar rashin ayyukan yi da matasan nahiyar ke fama da ita.

Daga karshe sharhin jaridun na fatan cewa, sakamakon babban taron zai kara bunkasa alakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China