Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taron manema labarai, Mr. Pyeong Chang ya ce suna maraba da zuwan kasashen duniya wannan gasa da kasar su za ta karbi bakunci. Ya ce tuni aka gudanar da gwajin kunna wutar bikin bude gasar, a wurin da aka fara gudanar da ita shekaru kimanin 2,500 da suka gabata.
Jami'in ya ce ya zuwa yanzu, an riga an kammala dukkanin ayyuka a filayen da za a gudanar da gasar, tun daga ranar 9 zuwa 25 ga watan na Fabarairu.
PyeongChang, ya ce burin su shi ne gasar ta Olympic ta bude wani sabon babi na hadin gwiwa tare da bunkasa wasanni. Ya ce kasancewar Sin za ta karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturu a shekarar 2022, sun fara hadin gwiwa da wakilan ta a fannin musayar kwarewa.
PyeongChang ya kara da cewa, gasar Olympic ta wuce batun wasa kadai, a ra'ayin sa batu ake yi na cudanyar al'adu, da musayar kwarewa a fannin Fasaha...ya ce " za mu iya musayar kwarewa...mun fara musayar matakan da suka dace a dauka... Za mu yi aiki tare domin tabbatar da nasara.
Daya daga kwararrun masu wasan zamiyar kankara na kasar Girka Apostolos Angelis, wanda aka zaba a matsayin wanda zai fara karbar fitilar gasar, ya nuna kyakkyawan fatan sa, na ganin cewa karin mutane sun shiga harkokin wasanni, domin amfana daga yadda wasannin ke kara kusanci tsakanin al'ummu daban daban.
A baya ma dai Angelis ya kasance mai jagorancin rike fitilar gasar da aka yi a biranen Sochi da Vancouver, sai dai wannan ne karon farko da zai jagoranci rikon fitilar a Olympia.
Tuni dai aka yi gwajin kunna wannan fitila mai tarihi, dake alamta bude gasar Olympic. Za kuma a kewaya da ita sassan kasar Girka daban daban, kafin mika ta ga mashirya gasar na kasar koriya ta kudu, a wani biki da za a gudanar a filin wasa na Panathinaic dake birnin Athens, ranar 31 ga watan nan na Oktoba.(Saminu Alhassan)