171025-Sabbin-zaunannun-membobin-ofishin-siyasa-na-kwamitin-tsakiya-na-JKS-sun-gana-da-yan-jarida-tare-zainab.m4a
|
Sabbin zaunannun membobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 sun hada da Xi Jinping, da Li Keqiang, da Li Zhanshu, da Wang Yang, da Wang Huning, da Zhao Leji, gami da Han Zheng. A gaban 'yan jarida na ciki da waje, babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping da ya sake zama mai rike da wannan mukami ya bayyana a madadin sabbin zaunannun membobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar cewa,
"A gun cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar, an zabi sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar, kana na ci gaba da zama matsayin babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, wannan aminci ne da aka nuna mini, kana kaimi ne da aka sanya gare ni. Na wakilci sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar, wajen nuna matukar godiya ga daukacin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, saboda imanin da suka nuna mana. Na kuma lashi takobin sauke nauyin da jama'a suka danka mana."
An tsai da wani muhimmin kuduri a gun babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19 da aka rufe a jiya Talata 25 ga wata, inda aka sanya "Tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki" a cikin kundin tsarin jam'iyyar. Kana an gabatar da shirye-shirye na makomar kasar Sin a gun taron. Xi Jinping ya bayyana cewa,
"Bayan da aka yi kokari a dogon lokaci, tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin ya shiga wani sabon zamani, biyowa bayan kokarin da aka dade ana yi, don haka ya kamata a bullo da sabbin abubuwa a wannan zamani, don samun sabbin nasarori. A shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta tabbatar da ganin an kafa zamantakewar al'umma mai matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni, a yayin da JKS ta cika shekaru 100 da kafuwa, tare da fatan ganin za a soma cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu na zamani mai wadata, da bin tsarin demokuradiya, da wayewar kai da kuma jituwa nan da shekara 2049. Wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin. Akwai wasu muhimman lokuta, yayin da ake gudanar da ayyuka, su ne lokacin da za mu fara aiki na musamman."
Wadannan muhimman lokuta sun hada da shekara mai zuwa, shekaru 40 ke nan tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da shekarar 2019, shekarar cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, da shekarar 2021, shekarar cika shekaru 100 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Xi Jinping ya jaddada cewa, manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, mataki ne da yake da muhimmanci matuka ga kasar Sin a wannan zamani. JKS za ta takaita fasahohinta, za kuma ta ci gaba da zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa, da inganta karfinta na tafiyar da harkokin kasa, tare da nacewa kan zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, a kokarin ganin matakan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje suna taimakawa cimma burin zaman rayuwa mai wadata, da amfani ga jama'ar kasar Sin, har ma ta kasa da kasa gaba daya. Xi ya bayyana cewa,
"Ya zama tilas 'yayan JKS su kasance masu kuruciya, da jagoranci, masu kishin kasa, kana da bauta wa jama'a har abada. Za a dauki tsauraran matakai na tafiyar da harkokin jam'iyyar daga dukkan fannoni, da aikin da ba shi da karshe."
Xi Jinping ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai manyan jam'iyyun siyasa fiye da 450 daga kasashe 165, wadanda suka aiko da sakwanni fiye da 800 na taya jam'iyyar murna da fatan alheri game da bude wannan taron. Game da hakan, Xi Jinping ya nuna matukar godiya a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya bayyana cewa,
"Al'ummar kasar Sin za su yi tsayin daka wajen kiyaye 'yanci da yankunan kasar, da tabbatar da zaman lafiya, gami da neman ci gaban kasa cikin lumana. Kana, za su himmatu tare da ragowar al'ummar kasashen duniya, domin raya duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil'adama, da kuma kara bayar da babbar gudummawa ga aikin shimfida zaman lafiya da neman ci gaba a duniya baki daya." (Zainab)