in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an kasashen Afirka sun yi sharhi kan rahoton taron JKS karo na 19
2017-10-24 10:57:44 cri

A cikin rahoton da babban sakatare Xi Jinping ya gabatar yayin babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 19 da ake shirin rufewa yau a nan birnin Beijing, ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya a fannin samar da kayayyaki, da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kana za ta kara kokari domin yaki da talauci a cikin gida da kuma da taimakawa kasashe masu tasowa, duk wadannan sun jawo hankulan jami'an gwamnatocin kasashen Afirka matuka.

Kwanakin baya wasu jami'an gwamnatocin kasashen Afirka kamar su jamhuriyar demokuradiyar kasar Congo da Mali da Benin da Madagascar suka zanta da manema labarai, inda suka jinjinawa abubuwan da babban sakatare Xi Jinping ya bullo da su a cikin rahoton da ya gabatar yayin bude babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19.

Game da kyautata matakan zuba jari ta hanyar yin kirkire kirkire domin sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasa da kasa a fannin samar da kayayyaki, jami'in ma'aikatar masana'antun jamhuriyar demokuradiyar kasar Congo Jules Nkiambi Kiese yana ganin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai taimakawa ci gaban kasashen Afirka, inda ya ce, "Kullum kasar Sin tana ba mu goyon baya, musamman ma a fannin fasahohi, hakan ya taimaka mana matuka yayin da muke kokarin samun ci gaba. Kasar Sin tana da karfin tattara kudi, kuma matsayin fasahohinta yana sahun gaba a fadin duniya, mu kasashen Afirka muna da albarkatun kasa masu tarin yawa, haka kuma ana iya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu zai taimakawa ci gaban kasashen Afirka."

Mataimakin daraktan cibiyar raya masana'antu ta kasar Mali Boubacar Traore ya bayyana cewa, wanann wani babban karfi a asirce a fannin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wajen samar da kayayyaki, jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen zai taimakawa ci gabansu, ya ce, "Karfafa hadin gwiwa a fannin samar da kayayyaki tsakanin kasashen duniya, wani abin albishiri ne a gare mu, muna da kayayyakin da suke bukatar gyarawa, kasar Sin tana da karfin tattara kudi, a saboda haka hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu zai amfanawa dukkan sassan biyu, ba ma kawai kasashen Afirka ne za su samu moriya ba, ita ma kasar Sin za ta amfana, banda haka jarin da kasar Sin ta zuba a kasashenmu zai taimaka mana wajen yaki da talauci, tare kuma da samun ci gaba."

Jami'in ma'aikatar kudi ta kasar Benin Mehdi Mama Yari ya bayyana cewa, yana fatan kasashen biyu wato Sin da Benin za su kara gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, inda ya ce, "Kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ta nagari ce ga kasashen Afirka, misali a kasarmu ta Benin, sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwa mai ma'ana a fannoni daban daban, nan gaba muna sa ran cewa, sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa a fannin aikin gona da fasaha da aikin gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da sauransu."

Kana Mehdi ya kara da cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen yaki da talauci, kamata ya yi kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su a wannan fannin.

Kan batun sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa domin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, jami'in ma'aikatar masana'antun kasar Madagascar Juducael Flavien ya bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar za ta samar da sabuwar dama ga kasashen Afirka wajen samun ci gaba, ya ce, "Ga kasashen Afirka, misali kasar Madagascar, hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' zai samar musu sabuwar damar samun ci gaba, yanzu kasar Sin tana bunkasa cikin sauri, muna son kara gudanar da hadin gwiwa tsakaninmu, saboda hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin zai samar da damar raya tattalin arziki a kasashen Afirka."

Mataimakin daraktan cibiyar raya masana'antu ta kasar Mali Boubacar Traore shi ma yana ganin cewa, hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" zai amfanawa daukacin kasashen Afirka.

Kana jami'in ma'aikatar kudi ta kasar Benin Mehdi Mama Yari ya bayyana cewa, Benin tana fatan za ta shiga shawarar bisa hanyar siliki kan teku ta karni na 21 saboda kasar Benin tana da tashar teku mai girma.

Game da kokarin da kasar Sin take na samar da taimako ga kasashe masu tasowa, jami'in ma'aikatar masana'antun jamhuriyar demokuradiyar kasar Congo Jules Nkiambi Kiese ya bayyana cewa, kasar Sin tana samar da taimakon ne ba tare da gindaya wani sharadi ba, wanan ya sa muka samu babbar moriya a zahiri.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China