Mista Wang wanda ke halartar babban taron wakilan JKS karo na 19 a nan Beijing, ya shaidawa taron manema labaru da aka yi a daren jiya a cibiyar watsa labaru na babban taron JKS,cewa an kaddamar da tsarin na Beidou ne a shekaru 1990. Kuma a ganinsa, an fara amfani da tsarin ne a kasar Sin, ana kuma kokarin fadada shi zuwa dukkan fadin yankin Asiya da tekun Pasific, da ma sassan duniya baki daya.
Mista Wang ya kara da cewa, a shekarun baya, an saba da yin amfani da tsarin tauraron dan Adam dake ba da jagoranci kan zirga-zirga yayin da muke yawo a cikin mota. Bayanan wurare da lokaci da irin wannan tsari yake samarwa suna samar mana da wani sabon salon na rayuwa kan yanar gizo. Yanzu wayoyin salula na zamani da dama na amfani da tsarin na Beidou da kuma a mabambantan sana'o'i. kuma ya yi alfahari da ganin hakan, a matsayinsa na mai aikin bunkasa tsarin. (Tasallah Yuan)