A cikin sakon da ya aiko, jagoran al'ummar Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce muhimmin rahoton da babban sakatare na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ba ma kawai ya bayyana babban burin da al'ummar kasar Sin ke son cimmawa ba ne, wato farfado da al'ummar Sinawa, da raya kasa har ta zama kan gaba a duniya, har ma zai samar da alfanu ga daukacin al'ummar duniya. Abbas ya kara da cewa, gudanar da babban taron cikin nasara, ya kafa alkibla ga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, domin jagorantar ayyukan raya kasar Sin a nan gaba.
Sa'an nan a nasa bangaren, shugaban Jamhuriyar Kongo, Denis Sassou-Nguesso ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da wani babban buri na raya duniya mai adalci da wadata, kuma sakamakon matukar kokarin da ta yi, jam'iyyar kwaminis din ta raya kasar Sin har ta zama abar koyi ga duk duniya baki daya.(Murtala Zhang)