in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci a sanya ido don dakile yaduwar cutar shan inna a Afrika
2017-10-25 09:49:03 cri

Jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana cewa, nahiyar Afrika a shirye take ta kawar da cutar shan inna wato polio muddin aka ci gaba da daukar matakai masu karfi irin wadanda ake amfani da su a halin yanzu ta hanyar daukar tsauraran matakan bincike, da yin riga-kafi, da kuma wayar da kan al'umma.

Daraktan hukumar ta WHO mai kula da kasashen Afrika Matshidiso Moeti, ya bayyana cewa, akwai yiwuwar mafi yawa daga cikin kasashen Afrika za su iya kubuta daga cutar nan da shekarar 2019 idan har suka ci gaba da daukar matakan kariya da kuma magance bazuwar cutar.

Moeti ya fada cikin wata sanarwa a Nairobi cewa, an samu gagarumin ci gaba a Afrika dangane da kawar da cutar shan inna, inda aka samu nasarar magance yawan bullar cutar daga 128 a fadin duniya a shekarar 2012, inda ya koma sau 4 a shekarar 2016.

A farkon wannan shekarar, shugabannin Afrika sun amince da wani ingantaccen shirin riga-kafi domin kawar da cutar shan inna.

Moeti ya ce, kasashen duniya sun sha alwashin goyon bayan kasashen Afrika da nufin kawar da cutar nan da shekarar 2019.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China