in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta cire Nigeriya daga kasashen dake fama da cutar shan inna
2015-10-27 09:49:07 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO a ranar Litinin din nan a hukumance ta cire sunan kasar Nigeriya cikin jerin kasashen dake fama da cutar shan inna, bayan da kasar ta yi nasarar samun tsaikon bular cutar har na tsawon watanni 15.

Domin tabbatar da wannan babban ci gaba, jami'ar hukumar mai kula da nahiyar Afrika Matshidiso Moeti da kanta ta sanar da wannan labari ga shugaban Nigeriya Muhammadu Buhari.

Madam Moeti wadda ta wakilci babbar daraktan hukumar Dr Margaret Chan, ta ce, tana farin cikin taya gwamnati da al'ummar kasar Nigeriya murnan samun tsaikon bular cutar, tare da sanar da cewar, an cire sunan Nigeriya a hukumance daga jerin kasashe masu fama da cutar.

Ta ce, wannan gaggarumin ci gaba wani tabbaci ne a kan yadda kasar ta kuduri aniya, daga gwamnati zuwa ga shugabannin al'umma da kuma hadin kai daga sauran kungiyoyi, abin da ke nuna yadda za'a iya samun ci gaba, muddin aka hada hannu waje daya domin samar da lafiya ga duniya baki daya.

Wannan irin nasarar da aka samu wajen yakar cutar shan inna a Nigeriya ta tabbata ne musamman ta yadda jihohi da kananan hukumomi suka ba da hadin kansu.

Madam Moeti ta kara da cewa, domin samun nasarar yakar cutar ta shan inna daga duk fannoni, dole ne a tabbatar da cewa, nan da shekaru 2 masu zuwa, ba a samun yaron da ya gurgunce ba saboda cutar. Babu lokacin da za'a yi saki jiki, dole ne a ci gaba da sa ido.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China