in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci majalisar dokokin Somaliya da ta taimaka don cimma muradun jama'ar kasar
2017-07-10 10:46:54 cri

Babban jami'in MDD a kasar Somalia ya bukaci 'yan majalisun dokokin kasar da su gudanar da ayyukan da za su tabbatar da cimma muradun al'ummar kasar Somaliyan ta hanyar amincewa da muhimman dokoki da za su tabbatar da bin doka da oda, da kuma karfafa tsarin mulkin demokaradiyya a kasar.

Wakilin musamman na sakatare janar na MDD a Somaliya, Michael Keating, wanda ya yi maraba da bude majalisar dokokin kasar ya bayyana cewa, tabbatar da cikakken ikon kasar Somaliya ya ta'allaka ne bisa yadda kasar ke dogaro da kanta a maimakon dogaro da wasu kasashe.

Cikin wata sanarwa da Keating ya fitar a Mogadishu, ya bayyana cewa, majalisar dokokin kasar ta Somaliya za ta ba da gagarumar gudunmowar ci gban kasar ne ta hanyar zartar da muhimman dokoki, ciki har da dokar da ta shafi zabe, da aiwatar da dokar da za ta ba da damar yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China