A fannin tabbacin zamantakewar al'umma, Yin Weimin ya bayyana cewa, a shekaru 5 da suka gabata, an kafa tsarin inshorar kiwon lafiyar tsofaffi mazaunan birane da kauyuka na kasar Sin, wanda ya samar da inshorar ga mutane fiye da miliyan 900, yawan mutane da suka karbi inshorar kiwon lafiya a kasar Sin ya kai fiye da biliyan 1 da miliyan 300, ana iya cewa, dukkan mutanen kasar Sin suna da inshorar kiwon lafiya a halin yanzu. (Zainab)