in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta nemi mambobin MDD su amince da yarjejeniyar haramta amfani da makaman nukiliya
2017-10-20 11:12:55 cri

A ranar Alhamis ne kasar Afrika ta kudu ta bukaci dukkan kasashe mambobin MDD da su sanya hannu kan yarjejeniyar haramta amfani da makaman nukiliya.

Kasar ta yi wannan kiran da babbar murya ne domin ceto al'ummun duniya daga fadawa cikin hadari da kuma illar da amfani da muggan makamai za su iya jefa rayuwar bil adama ciki.

Ministan makamashin kasar Afrika ta kudun David Mahlobo, ya shedawa wakilan dake halartar taron GIF na kasa da kasa karo na 44 a birnin Cape Town.

GIF, wani gamayyar hadin gwiwa ne na kasa da kasa wanda ke gudanar da bincike kan ci gaban da za'a iya samarwa a nan gaba ta hanyar amfani da makamashi.

A watan Yulin 2017, MDD ta amince da wata yarjejeniya game da haramta amfani da makaman nukiliya.

A watan jiya ne kasar Afrika ta kudu ta rattaba hannu kan yarjejeniyar. Gwamnatin kasar ta bayyana cewa, sanya hannun da kasar ta yi wata alama ce dake nuna irin yadda kasar ta nuna damuwarta game da samar da kyakkyawan muhalli ga bil adama ba tare da fuskantar barazanar makaman kare dangi ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China