in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar man Iraqi ta gargadi kamfanonin mai game da kulla yarjejeniya da yankin Kurdustan
2017-10-20 10:45:27 cri

Ma'aikatar man Iraqi, ta gargadi kasashen duniya da dukkan kamfanonin mai game da kulla yarjejeniya da yankin Kurdustan mai kwarya-kwaryar 'yancin kai, ba tare da samun izinin gwamnatin tarayyar kasar ba.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ruwaito ministan man kasar Jabbar Luaiby na cewa, duk wani yunkurin jami'ai da kamfanonin man kasashen waje na kulla yarjejeniyar da ta shafi man fetur a cikin kasar ba tare da samun izini daga gwamnati ba, kutse ne cikin harkokin cikin gidan kasar tare da take 'yancin mallakar yankinta da dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, gwamnatin tarayyar kasar da ma'aikatar man kasar, su ne kadai doka da shari'a suka ba damar kulla yarjejeniyar da ta shafi rayawa ko zuba jari a bangren albarkatun mai da iskar gas.

Ta kara da cewa, duk wani abu da ya sabawa hakan haramtacce ne, kuma ba shi da alaka da gwamnatin Iraqi, sannan gwamnatin da ma'aikatar man na da hakkin daukar matakin shari'a a kotunan dake ciki da wajen Iraqi domin kare arzikin kasar.

Sanarwar na zuwa ne, kwanaki kalilan bayan dakarun Iraqi sun kwace iko da rijiyoyi da bututan mai a yankin Kirkuk mai arzikin man fetur da wasu sassa da ake rikici kansu a yankin Kurdustan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China