in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da kwato birnin Mosul
2017-07-14 10:00:20 cri

Wata sanarwa da kwamitin tsaron MDD ya fitar, ta yi maraba da kwato birnin Mosul daga mayakan kungiyar IS, tana mai cewa, hakan babbar nasara ce a yakin da ake yi da ta'addanci.

Mambobin kwamitin na tsaro su 15, sun jinjinawa dakarun sojin kasar Iraqi bisa jajircewar su, wadda ta kai ga cimma wannan nasara ta fatattakar mayakan na IS.

Har wa yau kwamitin ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a Iraqi, da su tabbatar da kare rayukan fararen hula, yayin da dakarun kasar ke ci gaba da kakkabe gyauron mayakan na IS daga sauran kananan yankuna dake hannun su.

Daga nan sai mambobin kwamitin suka yaba da irin hadin gwiwar dake akwai tsakanin mahukuntan kasar da MDD, a yunkurin da ake yi na sake samar da daidaito a kasar, suna masu fatan za a yi aiki tare wajen cimma nasarar hakan.

A ranar Litinin ne dai aka ayyana 'yantar da birnin na Mosul, bayan shafe watanni 9 ana dauki ba dadi, wanda kuma hakan ya raba mayakan kungiyar ta IS da babbar tungar su ta karshe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China