Jiya Talata hukumar 'yan sandan kasar Iraki ta bayyana cewa, hukumar gudanarwar lardin Anbar dake yammacin kasar, ta karbi fararen hula kusan 1200, wadanda suka tsera daga yankin dake karkashin mamayen mayakan kungiyar IS.
Kanar Adel al-Dulaimi, na ofishin ba da umurni ga 'yan sanda na lardin Anbar ya bayyana cewa, fararen hular da karamar gwamnatin Rutba ta karba, sun fito ne daga garuruwan Aana, da Rawa, da kuma al-Qaim, kuma yawancinsu mata ne da yara kanana. Yanzu haka dai rundunar sojojin Iraki tana tantance mazan dake cikin wadannan fararen hula, domin tabbatar da babu mayakan kungiyar IS a cikin su. An kuma samar da abinci da wuri na tsugunarwa a sansanin.(Jamila)