in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraqi ta ce mayakan IS 300 ne suka rage a tsahon birnin Mosul
2017-07-06 09:51:25 cri

Kwamandojin sojin Iraqi sun bayyana cewa, a halin yanzu mayakan kungiya mai da'awar kafa daular musulunci IS 300 ne suka hallara a tsohon birnin Mosul, a lokacin da ake ci gaban da yin gumurzu a yammacin Mosul.

Manjo janar Sami al-Aaridhi, kwamandan cikin runduna mai yaki da ta'addanci CTS ya bayyana cewa, sun yi ammana cewa, a halin yanzu mayakan IS 300 ne suka rage, wadanda ake ci gaba da gwabzawa da su a wani karamin yanki dake kusa da kogin Tigris a tsohon birnin Mosul.

Haka zalika kwamandan CTS Abdul Ghani al-Asadi, ya shedawa 'yan jaridu cewa, dakarun sojin Iraqin suna ci gaba da dannawa zuwa karamin birnin da ya rage a hannun mayakan IS a tsohon birnin, kuma a halin yanzu ba su wuce nisan mita 250 daga gabar kogin Tigris din ba.

Asadi ya ce, fadan na ci gaban da yin kamari ne yayin da dakarun Iraqin ke ci gaba da fatattakar mayakan na IS daga waje mafi girma dake hannun mayakan na IS a tsohon birnin dake kusa da kogin Tigris, ya ce, a yanzu babban abin da ya ragewa mayakan na IS shi ne kaddamar da hare haren kunar bakin wake.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China