Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayyana babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC karo na 19 wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Beijing da cewa, tamkar bude wani sabon shafi ne, kuma a cewarsa kasar Rasha tana da wani babban tanadi game da hadin kan dake tsakaninta da kasar Sin.
Putin ya ce, suna matukar bibiyar yadda taron na CPC ke gudana, wanda a halin yanzu ya bude wani sabon babi. Da yake karin haske a wani taron tattaunawa da kwararru, mista Putin ya ce, an fuskanci wahalhalu kuma ana ganin alamun wasu damammaki.
Putin ya bayyana kasar Sin a matsayin kasa wacce ta daga darajar tattalin arzikin duniya baki daya. Duk da kasancewar tattalin arzikin GDP na kasar Sin ya dan ragu zuwa kashi 6.8 bisa 100 a rubu'in ukun shekarar 2017, sai dai ya yi amanna cewa, garambawul din da kasar ke tsarawa a halin yanzu zai samar da dawwamamman ci gaba.
Putin ya ce, suna da manyan tsare-tsaren yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin fasahar tauraron dan adam, da ci gaban kimiyya da kuma makamashi. Wadannan su ne manyan bangarorin da kasashen biyu za su gina dangantaka don tabbatar da ci gaban kasashen biyu.(Ahmad Fagam)