A ranar Alhamis babban sakatare Xi Jinping, ya bukaci mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC da kuma dukkannin kabilun kasar da su kara ciyar da gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin gaba a sabon zamanin da ake ciki.
Xi, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da wakilan jam'iyyar da suka fito daga lardin Guizhou wadanda suka zo don halartar babban taron CPC karo na 19.
Da yake nuna yabo dangane da irin ci gaban da lardin Guizhou ya samu cikin shekaru 5 da suaka gabata, Xi ya ce, tsarin gurguzu na al'ummar Sinawa ya shiga wani sabon matsayi.
Ya ce, wannan shi ne wani muhimmin hasashe game da sha'anin siyasa kuma alamu ne na irin tasirin da aka samu na dukkan muhimman tanade-tanaden da aka yi tun da farko.
Dangane da batun wanzuwar banbance-banbance a tsakanin al'ummonin Sinawa a bisa tarihi, wanda hakan ya shafi dukkan yankunan kasar, shugaba Xi ya fada a lokacin da ya jagoranci bude babban taron na CPC, inda ya tabo batutuwa masu sarkakiya tsakanin rashin daidaito da rashin ci gaba da kuma dunbun bukatun da al'umma ke da su na samun ingantacciyar rayuwa.
Xi ya fadawa wakilan na Guizhou cewa, dole ne a dauki dukkan matakan da suka dace domin kawar da matsalar rashin daidaito da rashin ci gaba don biyan muradun inganta rayuwar al'umma don su samu rayuwa mai inganci.(Ahmad Fagam)