in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta yi watsi da yarjejeniyar MDD ta kafa gwamnatin hadaka
2015-10-20 10:02:05 cri

Maalisar dokokin kasar Libya wacce ke samun amincewar kasashen duniya, a jiya Litinin ta yi fatali da bukatar da MDD ta gabatar mata ta neman a kafa gwamnatin hadaka a kasar.

Firaministan kasar Libya Ali Al-Tekbali, shi ne ya tabbatar da hakan, ya ce, lamarin ya faru ne yayin da mafi yawan 'yan majalisar dokokin suka goyi bayan watsi da waccar bukata ba tare ma da sun kada kuri'a ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar Libya ya rawaito cewar, an jiyo wasu 'yan majalisar na cewa, majalisar dokokin kasar ta dauki wannan mataki ne bayan da ta lura cewar, an samu cin karo da juna a cikin bayanan da ke kunshe a daftarin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu kansa tun da farko.

A hannu guda kuma, majalisar dokokin kasar bangaren 'yan adawa ba su ce uffan ba kan bukatar MDD.

Amma majalisar Libya ta daban a Tripoli ba ta nuna ra'ayinta ba kan batun tukuna.

Shugaban tawagar jami'an MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Libya Bernardino Leon, ya ba da sanarwa a ranar 8 ga wannan wata cewar, bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Libya, sun amince su shiga shirin gwamnatin hadin kan kasa bayan shekara guda ana tattauna hanyoyin da za'a warware rikicin kasar. (Ahmad Fagam )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China