Shugaba Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da daidaikun mutane, da kungiyoyin wasanni na kasar Sin, wadanda suka kunshi kwararru da kuma matsakaitan 'yan wasa, tare da wadanda suka samu lambobin yabo yayin manyan wasannin kasar.
Ya ce, wasanni na samar da wani dandali na kafuwar kasa mai karfi da ci gaba, don haka kamata yayi a baiwa batun ciyar da bangaren wasanni gaba muhimmanci, ta hanyar kara kokari wajen shiryawa da aiwatar da sabbin ayyuka a fannin.
Yayin ganawar, Shugaba Xi ya ce, an samu gagarumin ci gaba a bangaren wasanni cikin shekaru 5 da suka gabata, ciki har da habakar shirin 'lafiyar jiki ga kowa', da nasarorin da aka samu a wasannin da ake yi a duniya, da kara zurfafa sauyi a bangaren, tare da damar karban bakuncin wasanni motsa jiki da za a yi a lokacin hunturu a shekarar 2022.
Ya ce bunkasa wasanni na cikin kudurori da kasar ke fatan cimmawa, karkashin manufofin ci gaban kasar da aka zartas, yayin taron JKS na 18 da ya gudana a shekarar 2012.Ana dai fatan aiwatar da sabbin dabaru, da dunkule harkokin wasannin na gama gari, da na gasanni.
An dai bude gasar wasannin da ake gudanarwa duk bayan shekaru hudu hudu ne a Lahadin karshen kamo, da gakarumin bikin da shugaba Xi ya halarta. Baya ga shugaban na Sin, taron ya kuma samu halartar manyan baki da dama, ciki hadda shugaban kwamitin shirya gasannin Olympic na kasa da kasa Thomas Bach. Za kuma a gudanar da gasannin da aka tsara ne a birnin na Tianjin zuwa ranar 8 ga watan Satumbar dake tafe.(Saminu Alhassan)