in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahar gina jiki
2017-08-15 15:06:43 cri

Gina jiki ko tara kwanji, na cikin bangaren motsa jiki, wato ya shafi yadda ake kokarin rage kiba, tare da neman samun karin tsoka da kwanji a jikin dan Adam, ta yadda za a samu suffar jiki mai kyau.

Wannan fasaha a halin yanzu tana farin jini sosai a nan kasar Sin, ganin yadda a duk wata unguwar birni, ba a rasa dakin "gym", wato wurin motsa jiki daya ko biyu. Sa'an nan duk inda ka leka, a kan ga mutane da suna tallace-tallace ga jama'a domin su yi rajista a daya daga cikin dakunan Gym din. Da ka shiga cikin irin wadannan dakuna na Gym, za ka ga akwai na'urorin motsa jiki daban daban, akwai nau'in ta gudu a wuri guda, da sauran na'urori masu nauyi, da za su taimakawa motsa sassan jikin mutum daban daban, da wurin ninkaya, da dai sauransu. Sa'an nan, jama'ar kasar Sin, musamman ma matasa da samari, da 'yan mata masu neman siffar jiki mai kyan gani, suna zuwa dakunan motsa jiki na Gym a kai a kai.

Da ka je Gym, musamman ma da maraice, wato lokacin da aka tashi daga aiki, to, za ka ga wurin cike yake da mutane. Wasu suna gudu, wasu suna kokarin daga na'urori masu nauyi, wasu suna rawar musamman ta motsa jiki, wasu suna taka keken iri na musamman domin kara karfin kafa, yayin da wasu kuma ke wasan ninkaya. Wadannan mutane suna da sana'o'i daban daban, wasu dalibai ne, wasu suna aikin ofis, wasu tsoffi ne da suka yi ritaya, amma dukkansu suna da burin gina jikinsu, don tabbatar da lafiyar jiki, da samun siffar jiki mai kyau.

Shaidar tarihi ta nuna mana cewa, a wasu tsoffin dauloli irin su Masar, da Girka, da daular Tamilakam dake kudancin kasar Indiya ta yanzu, an riga an samu mutanen da suka fara daga abubuwa masu nauyi don gina jikinsu. Amma ba a fara samun fasahar gina jiki ta zamani ba tukuna, sai zuwa shekarun 1800. A lokacin, akwai wani dan kasar Jamus mai suna Eugen Sandow, wanda ya yi kokarin yayata fasahar gina jiki a kasar Birtaniya. Mista Sandow yana da tsarin jiki mai kyau, kuma ya yi amfani da fasahar gina jiki wajen samun tsoka da kwanji da yawa a jikinsa. Daga bisani, ya kan sanya bante ya hau dandali domin nuna tsarin jikinsa ga jama'a. A lokacin jama'a ba su taba ganin irin wannan aikin da ya yi ba, suna mamakin yadda wani mutum zai iya samun jiki mai tsoka da yawa kamar haka. Lamarin da ya sanya Eugen Sandow ya yi suna. Daga bisani ya bude wasu kamfanonin samar da na'urorin motsa jiki, har ma sunansa ya zama tambari ga wasu na'urorin motsa jiki da aka samar.

Zuwa shekarar 1901, Sandow ya kafa gasar gwada fasahar gina jiki ta farko a duniya, gasar da ta gudana a birnin London na kasar Birtaniya. Inda aka baiwa mutumin da ya ci gasar wata babbar kyauta, wato wani mutum-mutumi na zinariya da siffarsa ta yi kama da ta Sandow. Amma zuwa yanzu mutane sun fi sanin mutum-mutumi na Sandow na tagulla, domin ya kasance kyautar yabo da ake baiwa Mista Olympia, wato wanda ya lashe kambi a babbar gasar fasahar gina jiki ta duniya.

Zuwa shekarun 1950 sannu a hankali fasahohin gina jiki sun fara samun karbuwa sosai, musamman ma tsakanin kasashe dake yammacin duniya. A lokacin ana samun manyan gasanni a wannan fanni, da mujallar musamman mai gabatar da fasahohin gina jiki, da ingatattun dabarun da ake bi a fannonin cin abinci, da motsa jiki, domin kara samun tsoka da kwanji. Karkashin wannan yanayi ne aka fara samun wasu manyan hukumomi na kasa da kasa masu kula da aikin yayata fasahohin gina jiki, ga misali, International Federation of Bodybuilders (IFBB), wato hadaddiyar kungiyar 'yan wasa masu fasahar gina jiki, da Amateur Athletic Union (AAU), wato hadaddiyar kungiyar matasan 'yan wasa, da dai sauransu. Wadannan hukumomi, a nasu bangaren, sun sa kaimi ga yunkurin samun karin manyan gasanni ta fuskar fasahar gina jiki. Yanzu akwai manyan gasanni da ake ba su taken "Mista wani wuri", ga misali, idan gasar da ta gudana a kasar Amurka ne, sai a ce "gasar mista Amurka". Sa'an nan gasannin fasahar gina jiki da suka fi shahara su ne, gasar mista World, wato mista duniya, da ta mista Olympia. An kafa gasar mista Olympia a shekarar 1965, karkarshin sa ido na hukumar IFBB. Zuwa yanzu gasar ta kasance mafi tasiri a duniya a fannin fasahar gina jiki.

Ta fuskar zaman rayuwarmu na yau da kullum, za a iya ganin amfanin fasahar gina jiki ga lafiyar jiki na kowa. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane, musamman ma matasa, suke kokarin zuwa dakunan Gym don motsa jikinsu. Bari mu kidaya abubuwa masu kyau da za a iya samu bisa daukar fasahar gina jiki. Da farko dai, dabarun a wannan fannin sun nuna mana hanyar daidaita cin abinci, da motsa jiki, gami da hutu. Ka san mutum ba zai samu lafiyar jiki ba, in har bai yi kokarin samun daidaito tsakanin cin abinci da motsa jiki ba, da kuma hutu. Ta hakan, mutum zai kai ga kokarin magance sharar abinci, da rungumar abinci masu gina jiki, tare da motsa jiki a kai a kai, da samun isashen hutu. Sannu a hankali za ka ga tsarin jikin mutumin ya canza, ya fara samun karin karfin jiki, kuma ba ya saukin kamuwa da cuta.

Amfanin fasahar gina jiki na biyu shi ne za ta taimakawa rage kiba. Ka san idan an dauki fasahar gina jiki, to, zai sa tsoka da kwanji su karu a jikin mutum. Kuma karin tsokar za ta shanye sukari dake cikin jinin mutum, hakan zai hana sukari ya tsaya a jikin mutum ya zama kiba. Ka san cututuka da yawa, wadanda ke haifar da illa ga zuciya da hanyar jini, an tabbatar suna da alaka da kiba. Don haka rage kiba shi ma wani babban amfani ne ga lafiyar jikin dan Adam.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China