in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a watsa bikin bude babban taron JKS karo na 19 gobe kai tsaye ta hanyoyi daban daban
2017-10-17 13:25:51 cri
Gobe Laraba 18 ga wata da karfe 9 na safe ne za a bude babban taron jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Za a watsa bikin bude taron kai tsaye ta gidan rediyon CNR na kasar Sin, gidan telibijin na kasa CCTV, gidan telibijin na CGTN na kasar Sin da gidan rediyon kasar Sin wato CRI cikin harsunan Sinanci, Turanci da Rashanci. Haka kuma, za a watsa labaru ne game da bikin bude taron a tasoshin yanar gizo na www.people.com.cn, www.xinhuanet.com, http://www.cctv.com, da www.china.com.cn, da manhaja jaridar People's Daily, kamfanin dillancin labarun Xinhua da CCTV ta wayar salula. Har ila yau, gidajen telibijin, da gidajen rediyo dake kananan hukumomin kasar Sin su ma za su watsa bikin bude taron kai tsaye. (Tasallah Yuan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China