A yayin da yake zantawa da manema labaru, Schack ya ce, Isra'ila ta fara kafa shinge a zirin Gaza tun a shekarar 2007, kuma a cikin shekaru uku da suka wuce, an rufe sashen bakin teku dake iyaka tsakanin Gaza da Masar a tsawon lokaci.
Bisa wannan yanayi da ake ciki, masatan yankin za su iya rasa imani game da makomarsu, hakan kuma na iya sanya su kara shiga wasu ayyuka na laifuka, da kara fuskantar barazana ta fadawa yanayin son nuna karfin tuwo. (Bilkisu)