in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yanke shawarar dakatar da taimakawa Palasdinawa da suka  rasa muhallansu
2015-01-28 15:15:35 cri

Hukumar samar da agaji ta MDD ta yanke shawara ta dakatar da agaji yayin da Isra'ila ta kai farmaki a zirin Gaza a watan Yuli da Agustan shekarar bara.

Hukumar wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta ce, ta yanke shawarar hakan ne saboda karancin kudaden da hukumar ta samu daga Larabawa da kuma masu bayar da taimako na kasashen ketare.

Sanarwar wacce aka gabatar a yayin wani taron kwanaki 2 na masu bayar da agaji, ta ce, Paladinawa ba su ji dadin dakatar da taimakon da ake ba su ba, kuma hakan zai sa tilas iyalai da yawa su tare a cikin cibiyoyin agaji na kungiyoyin kasashen ketare.

Hukumar samar da agajin ta MDD ta ce, ta samu guddumuwar dalar Amurka miliyan 135 daga cikin dalar Amurka miliyan724 da kasashe suka yi alkawarin za su bayar a taron masu bayar da agaji na duniya wanda aka yi a Masar a watan Oktobar shekarar bara.

Hukumar agajin ta MDD ta ce, tun farko ta baiwa iyalan Palasdinawa kimanin dubu 66, adadin kudi har dalar Amurka miliyan 77 domin su gyara gidajensu da aka wargaza ko kuma su biya kudin haya.

Shugaban hukumar bayar da agajin ta MDD Robert Turner, ya ce, har yanzu wasu iyalai suna zama a cikin buraguzan gidajensu da aka lalata kuma hakan yana da hadarin gaske saboda lokaci ne da ake yin kankara kuma tuni har wasu yara sun fara mutuwa saboda tsananin sanyi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China