Sarki Mohammed na VI na Morocco, da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, sun sha alwashin bunkasa huldar kawance dake tsakanin kasashen su.
Yayin wata zantawa da suka yi ta wayar tarho a jiya Litinin, shugabannin biyu sun ce za su fadada dangantakar su a dukkanin sassa, tare da tabbatar da an aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimma, yayin ziyarar da sarkin na Morocco ya kai Abuja, fadar mulkin Najeriya a bara. Wata sanarwa da fadar sarkin na Morocco ta fitar, ta bayyana cewa, yarjeniyoyin sun shafi batun inganta harkar noma, da samar da takin zamani, da kuma hadin gwiwa a fannin tsaro.(Saminu)