in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamandan sojin Libya ya ce ba zai halarci taron AU kan kasar ba
2017-09-08 09:12:04 cri

Kwamandan sojin Libya dake gabashin kasar Manjo Janar Khalifa Haftar, ya ce ba zai halarci taron tarayyar Afrika kan rikicin kasarsa da za a yi a Brazzaville na Congo ba.

Kasar Congo ce za ta karbi bakuncin taron na ranar Asabar da shugaban kasar Denis Nguesso ya dauki nauyi, wanda kuma shi ke jagorantar kwamitin tarayyar kan batun Libya.

Manufar taron ita ce, shawo kan matsalolin siyasa da ke tarnaki ga aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da MDD ta gabatar tare da mara baya ga yunkurin cimma sulhu a kasar.

Tun a ranar Laraba da ta gabata shugaban majalisar dokoki dake gabashin kasar Aqila Saleh ya isa birnin Brazzaville don halartar taron. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China