in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ba ta da wata manufa a Libya face cimma hadin kai da tsaro
2017-08-28 10:28:18 cri

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya ce kasarsa ba ta da wata munufa a Libya da ya wuce cimma tsaro da kwanciyar hankali da hadin kan al'ummar kasar.

Omar Al-Bashir na wannan jawabi ne yayin wani taron manema labarai, bayan ya kammala tattaunawa da shugaban gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya wato Fayez al-Sarraj a birnin Khartoum.

Shugaban ya ce, yanayin rashin kwanciyar hankali da Libya ke ciki na tasiri a kan Sudan. Inda ya ce, suna kashe kudi mai yawa wajen magance matsalar shige da fice ba bisa ka'ida ba da safarar bil adama da laifuffukan da ake aikatawa a kan iyakoki.

Shugaba Al-Bashir ya kara da cewa, ba su da wani muradi da ya wuce cimma kwanciyar hankali da zaman lafiya da tsaro da hadin kan al'ummar Libya.

A nasa bangaren, Fayez al-Sarraj, ya ce ziyararsa a Sudan wani bangare ne na tsarin tuntubar kasashe 'yan uwa.

Ya ce, sun tattauna da shugaba Al-Bashir game da yadda za a tabbatar da tsaron iyakoki da kuma inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, Sudan muhimmiyar makociya ce kuma za su aiki tare wajen inganta huldar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China