in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta haramtawa Amurkawa shiga kasarta a matsayin martani
2017-09-28 10:31:32 cri

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Libya ta ba da sanarwa a ranar Laraba, inda ta haramtawa 'yan kasar Amurka shiga kasarta, a matsayin martani ga matakin da shugaban Amurkar Donald Trump ya dauka na haramtawa 'yan kasar Libyan shiga Amurkar.

Gwamnatin Libya ta bayyana matakin da kasar Amurkar ta dauka a matsayin mummunan tada hankali ga 'yan kasar ta Libya, inda ta zargi Amurkar da mayar da 'yan kasar Libyan matsayin 'yan ta'adda, duk da kasancewar dakarun sojin kasar Libya na ci gaba da fafutukar yakar 'yan ta'adda tare da tallafin jama'ar kasar ta Libya.

Matakin da Amurka ta dauka ya sa gwamnatin rikon kwaryar ta Libya ba ta da wani zabi face mayar da martani na haramtawa 'yan Amurka shiga kasar Libyan.

A ranar Litinin ne ofishin jakadancin Amurka ya sanar da haramcin baiwa 'yan kasar Libyan izinin shiga Amurka a bisa dalilai na tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China