Jami'ai 47 masu kula da harkokin kauyuka da aikin gona wadanda suka fito daga kasashen Afirka 13, wato Algeria da Benin da Brundi da Kamaru da Kongo Brazaville da Kongo Kinshasa da Cote D'Ivorie da Senegal da Mali da Guinea da Djibouti da Senegal ne suka yi nazarin.
Yayin kwas din, an cudanya ta hanyoyi daban daban da jami'an na kasashen Afirka, kan manufofin raya kauyuka da aikin gona na kasar Sin, da yadda kasar Sin ke kokarin kawar da talauci da yin kwaskwarima kan tsarin kauyuka, da kyautata yanayin halittu a kauyuka da manufar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin aikin gona da kauyuka da kuma nasarorin da aka samu.
Har ila yau, jami'an sun kai ziyara ga wasu iyalai manoma, inda suka gano yadda ake samun ci gaban aikin gona. Baya ga haka, sun yi bincike a wasu yankunan kasar Sin, don fahimtar yadda ake samun ci gaban kauyuka, inda suka fahimci hakikanin yanayin da wurare daban-aban na kasar Sin ke ciki, wajen raya aikin gona da samun ci gaban kauyuka. (Bilkisu)