in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin a idon wata malamar jami'a ta kasar jamhuriyar Congo
2017-10-12 11:49:17 cri


Jami'ar Marien Ngouabi jami'a ce mai mallakar gwamnati daya tak ta jamhuriyar Congo. A ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki a kasar Congo a wancan lokacin, ya gana da shugaban kasar Denis Sassou Nguesso, sun halarci bikin kaddamar da wani sabon dakin karatu da wani dakin nuna al'adun kasar Sin a cikin jami'ar, wadanda kasar Sin ce ta ba da kudi domin gina su. A lokacin ne, shugaban kasar Sin ya yi hira da Ai Jia, wata malama 'yar kasar Congo dake koyar da yaren Sinanci a cikin jami'ar. Zuwa yanzu, shekaru 4 ke nan suka wuce, duk da haka, malamar ta ce ta kan tuna da hirar da ta yi tare da shugaban, tamkar wani abu ne da ya faru a jiya.

Hakika Ai Jia ita ce sunan malamar cikin Sinanci, yayin da ainihin sunanta shi ne Edwige Kamitewoko. Ta taba kwashe shekaru 4 tana karatu a jami'ar Zhejiang ta kasar Sin, inda ta samu digiri na 3 ta fuskar ilimin tattalin arziki. Daga bisani ta koma kasar Congo, ta fara koyar da ilimin tattalin arziki da Sinanci a jami'ar Marien Ngouabi. Yayin da take tunawa da rangadin da shugaba Xi Jinping da shugaba Denis Sassou Nguesso suka yi a jami'arta, ta ce wannan lamari ne mai burgewa.

"Gaskiya wannan batu ya burge ni kwarai! Da wuya ne a samu wannan dama! Abin da ya sa na yi murna sosai. Shugaba Xi Jinping ya tambaye ni a ina ne na koyi harshen Sinanci? Na ce a Hangzhou. Sai ya tambaye ni na yi karatu a can daga yaushe zuwa yanshe? Na amsa cewa, daga shekarar 2001 zuwa ta 2005, wato na kwashe shekaru 4 ina karatu. Daga bisani ya ce ko kina son Hangzhou? Na ce ina kaunar birnin, saboda shi ne wani wuri mai kyau. Ya ce a lokacin shi ma yana aiki a Hangzhou, sai dai ba mu taba gamuwa da juna ba."

Har yanzu Ai Jia ta kiyaye hotunan da aka dauka yayin da take hira da shugabannin 2. Ta ci gaba da tunawa da abin da ya faru a waccan rana cewa:

"Shugaba Xi Jinping ya tambaye ni, malaman makarantar Confucius 'yan Congo ne ko Sinawa ne? Na ce akwai malamai Sinawa 2, da malama 'yar Congo daya, wato ni. Ya ce muna da malamai masu kwarewa da yawa, maganar da ta burge ni sosai, ta sa na yi alfahari. Na yi zumudi sosai a lokacin, har ma ban san me zan fada ba. Shugaba Sassou shi ma ya tambaye ni tun daga yaushe na fara koyar da Sinanci? Na ce shekaru 6 da suka wuce. Ya ce, shekaru 6? Bai yi tsammanin na dade ina wannan aiki kamar haka ba. Abin da ya faranta masa rai, ya kuma karfafa mana gwiwa don na ci gaba da kokarin aiki."

Zuwa yanzu, ban da kula da ayyukan koyar da ilimin tattalin arziki da Sinanci, ita Ai Jia tana da mukamin darektan sashen huldar dake tsakanin kasa da kasa, kuma tana mai da hankali kan abubuwan da suka faru a kasar Sin. A ganinta, kasar Sin tana ci gaba cikin sauri karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping.

"Shugaba Xi yana cike da imani, kana yana kula da ayyuka cikin tsanaki. Ra'ayoyinsa sun yi daidai, don haka ina sonsa sosai. Mutumi ne da ya iya yanke shawara cikin sauri, kuma ya taba aiki a matsayin jami'i na matakai daban daban. Irin ci gaban da kasar Sin ta samu yana da burgewa, har ma ya zama wani misali ga yunkurin raya tattalin arziki. Mu ma ya kamata mu koyi fasahar kasar Sin, domin mu raya kasarmu ta Congo."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China