in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum guda ya jikkata sakamakon fashewar wani abu a ofishin IMF ake Paris
2017-03-16 20:27:05 cri
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa, na cewa wani mutum guda ya jikkata, sakamakon fashewar wani abu dake kunshe cikin wata wasika, a ofishin asusun IMF da ke birnin na Paris a yau alhamis.

An ce mutumin ya samu kuna a hannuwansa da kuma fuskarsa, yayin da ya bude wasikar, kamar dai yadda kafofin watsa labaran birnin suka tabbatar. Sai dai rahotannin sun ce fashewar ba ta shafi wani bangare na ginin ofishin ba.

An ce tuni 'yan sanda suka fara shirin binciken musabbanin aukuwar wannan lamari.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China