Cibiyar dai za ta iya kokarinta, wajen taimakawa manema labarai daga yankunan Hong Kong da Macau, gami da Taiwan, da na sauran kasashe, wajen samun katunan izinin watsa labarai. Wani aiki na daban da cibiyar za ta yi shi ne, gudanar da taron manema labarai, da samar da taimako ga manema labarai, don su samu damar bada rahotanni game da babban taron.
Har wa yau, cibiyar za ta bude tashar Intanet, da kuma wallafa bayanai ta kafar manhajar WeChat, domin samar da hidimar fasaha da bayanai ga manema labarai a yayin babban taron dake tafe a wata mai zuwa.
'Yan jaridun kasashen ketare za su iya tuntubar wasu lambobin waya don samun taimako, wato+861068576100, +861068576200, da kuma +861068576300. (Murtala Zhang)