Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga al'ummomin duniya su yi yaki da cin zarafin mata a lokutan da ake rikici ta hanyar magance abubuwan dake haifar da matsalar tun daga tushe.
A jawabinsa domin ranar kawar da cin zarafi a lokutan rikici ta duniya, Antonio Guterres ya ce, fyade da cin zarafi dabaru ne na ta'addanci da yaki, da ake amfani da su wajen wulakantawa da lalatawa da kuma zubar da darajar mata, wanda kuma ake amfani da su a fafutukar kare dangi.
Ya ce, MDD na iya kokarinta na ganin ta magance abubuwan dake haddasa cin zarafin mata a lokutan rikici ta hanyoyin diflomasiyya da samar da zaman lafiya da karfafawa kasashe daukar matakai da kuma kawo karshen wariyar jinsi.
A ranar 19 ga watan Yunin 2015 ne babban zauren MDD ya amince da kudurin ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata a lokutan rikici. (Fa'iza Mustapha)