in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta yaba da rawar da Sin ke takawa a harkokin sararin samaniya
2017-09-28 13:25:53 cri

Babbar darektar ofishin MDD mai kula da harkokin sararin samaniya Simonetta Di Pippo, ta yaba da gagarumar rawar da kasar Sin take takawa a kwamitin majalisar mai kula da yadda kasashe ke amfani da sararin samaniya cikin lumana.

Di Pippo ta bayyana wadannan kalamai ne, cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin taron harkokin zirga-zirgar sararin samaniya na kasa da kasa karo na 68, wanda aka bude ranar Litinin a birnin Adelaide dake kudancin kasar Australia.

Jami'ar ta yaba musamman da kokarin kasar Sin na bude sararin masaniyar ga kowa da kowa, musamman kasashe masu tasowa ta hanyar yin hadin gwiwa da ofishinta

Ta ce, tana fatan kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a tsarin binciken falaki, ciki har da harba kumbon binciken sararin samaniya maras matuki a wasu lokutan kuma har da bil adama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China