in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban UNGA yana fatan Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa
2017-09-14 09:43:19 cri

Shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajcak ya ce, yana fatan kasar Sin za ta kara taka gagarumar rawa a harkokin kasa da kasa.

Mirosav wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya ce hakika a shirye kasar Sin take ta taka muhimmiyar rawa a harkokin MDD, duba da yadda take shiga a dama da ita a ajandar majalisar ta samar da dauwamamman ci gaba nan da shekara 2030.

Ya ce, duk da irin ci gaba da aka samu a fannin farfadowar tattalin arzikin duniya, har yanzu kasar Sin tana ci gaba da kara zuba jari a kasashe masu tasowa, lamarin da ya janyo hankulan kasashen duniya baki daya. Kana baya ga kasancewarta wakiliyar din-din-din a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin tana daga cikin kasashen dake sahun gaba wajen ba da gudummawar kudi ga majalisar, da ma kudaden raya kasashe da majalisar ke tafiyarwa.

Ya ce, gudummawar da kasar Sin ta ba da wajen kafa gidauniyar nan ta zaman lafiya da raya kasa ta dala biliyan 1 ta Sin da MDD nan da shekaru 10 masu zuwa, ta taimaka matuka. Ya ce, ya ji dadin yadda kasar Sin ta kuduri aniyar shiga rundunar tabbatar da zaman lafiya ta MDD da kuma nuna misali wajen kafa rundunar 'yan sandan tabbatar da zaman lafiya ta din-din-din, baya ga wasu dakarun tabbatar da zaman lafiya na kota kwana guda 8,000 da kasar Sin ta kafa.

Jami'in na MDD ya ce, kasar Sin tana daga cikin kasashe na farko da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris, matakin da ya kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China