in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana yawon bude ido da Sinawa ke yi a wasu kasashe a matsayin gaggarumin ci gaba
2017-05-10 10:13:37 cri

Hukumar kula da yawon bude ido ta MDD UNWTO ta bayyana gudunmuwar da Sinawa ke badawa a baya-bayan nan, ga kasuwar yawon bude ido a duniya, a matsayin gaggarumin ci gaba.

Daraktan hukumar a yankin Asiya da Pasific Xu Jing, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, karuwar adadin Sinawa dake kai ziyara wasu kasashe gaggarumin ci gaba ne, inda ya yi tsokaci kan kudaden da aka kashe a bara, wanda ya nuna cewa, Sinawa masu yawon bude ido sun kashe karin kashi 12 cikin dari na abun da suka kashe a shekarar 2015.

Alkaluman hukumar ta UNWTO sun nuna cewa, Sinawa masu yawon bude ido sun kashe dalar Amurka biliyan 261 a kasashen da suka je, yayin da adadin masu yawon bude ido a kasashen waje ya karu da kashi 6 zuwa miliyan 135 a bara.

Xu Jing ya ce, gudunmuwar Sinawa za ta ci gaba da inganta zamantakewa a duniya, yana mai cewa, la'akari da cewa Sinawan na amfani da kafar intanet wajen kama wuraren da za su sauka, alama ce dake nuna cewa, suna zuwa lunguna fadin duniya da ba a san su ba sosai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China