in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kare hakkin bil-Adam ta MDD ta amince da kudurin da Sin ta gabatar
2017-06-23 09:34:48 cri

A jiya ne hukumar kula da kare hakkin bil-Adama ta MDD ta amince da wani kudurin da kasar Sin ta gabatar mai taken "gudummawar ci gaba ga jin dadin 'yancin kowa da kowa". Wannan dai shi ne karon farko da hukumar ta amince da wani kuduri game da batutuwan da suka shafi ci gaba.

Shi dai wannan kuduri da kasar ta Sin ta gabatar ya mayar da hankali ne ga fatan kasashen duniya na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil-Adama tare da tabbatar da cewa, ci gaba ya taka muhimmiyar rawa ga cin gajiyar duk wani 'yanci na rayuwar bil-Adama.

Kudurin ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su yi la'akari da ci gaban da ya shafi jama'a, wanda jama'a suka samar kuma domin jama'a. Haka kuma, kuduri ya bukaci kasashen duniya da su karfafa hadin gwiwar kasa da kasa tare da yayata bukatar samun dawamamman ci gaba, musaman yayin da ake aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. Domin ta haka kawai dan-Adam zai amfana da duk wani 'yanci ko hakki da ake ikarari.

Bugu da kari, kudurin ya yi kiran da a kara himmatuwa wajen yayata matakan raya kasa da nufin karfafa hadin gwiwa, da samun moriyar juna da koyi da fashohin juna.

Kasashe sama da 70 ne suka goyi bayan wannan kuduri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China