in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka wani babban jami'in tsaron Libya
2017-07-10 10:08:32 cri

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba, sun kashe kanal Abdurrazzag E'mesh, babban jami'in tsaron birnin Gharian na kasar Libya a ranar Lahadi.

Wata majiya daga jami'an tsaron kasar ta sanar da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, babban jami'in na birnin Gharian, Col. Abdurrazzag E'mesh, ya game da ajalinsa ne tun a ranar Lahadi lokacin da wani mutum dauke da makami ya bude masa wuta, inda ya hallaka shi nan take.

An kashe E'mesh ne a kofar gidansa. Majiyar ta kara da cewa, kawo yanzu ba'a gano mutumin da ya yi kisan ba.

Kasar Libya ta fada cikin halin tabarbarewar tsaro ne tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi daga karagar mulkin kasar a shekarar 2011. Tun daga wancan lokaci ne ake ci gaba da samun kashe kashen rayukan jama'a, babu kakkautawa a kasar ta arewacin Afrika.

Birnin Gharian, yana da tazarar kilomita 80 dake kudancin babban birnin kasar Tripoli, sai dai yankin yana da karancin rikici, kuma akwai kwanciyar hankali idan aka kwatanta da wasu yankunan kasar, sakamakon dalilai na fahimtar juna a tsakanin kabilun yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China