in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Najeriya da ta rage yawan kudin ruwa
2016-11-29 11:06:18 cri

An yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta rage yawan kudin ruwa na manufar kudinta da kashi 14 cikin 100 domin tabbatar da bunkasuwa a cikin bangaren masana'antu.

Sai a yayin da za a rage yawan kudin ruwa ne cewa masu masana'antu za su iya rike da bunkasa masana'antunsu, kuma a lokacin faduwar tattalin arziki, in ji Frank Jacobs, shugaban kungiyar masu masana'antun Najeriya a ranar Litinin a birnin Lagos, yayin wani dandalin tattalin arzikin Najeriya.

Mista Jacobs ya kara da cewa, tare da matakan da suka dace, bangaren masana'antu zai iya janyo wani canza ga salon tattalin arziki, ya jaddada cewa, rike yawan kudin ruwa zai iya janyo matsala ga bunkasuwar bangaren masana'antu.

A cewarsa, adadin kudin ruwa na kashi 14 cikin 100 ba zai karfafa bunkasa kayayyakin da ke sarrafawa cikin gida ba. Rike adadin yanzu zai hana bangaren da ya fuskanci mastalar ja da bayan tattalin arziki, in ji jami'in.

Babban gwamnan bankin Najeriya, mista Godwin Emefiele, ya sanar a makon da ya gabata matakin rike adadin da kashi 14 cikin 100.

Baya ga rike wannan mataki, mista Emefiele ya bayyana cewa, kwamitin ya kuma jefa kuri'ar amincewa da rike rabon tsabar kudin ajiya da kashi 22,5 cikin 100. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China