in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kayyade yawan mutane da gine gine da za su wanzu a birnin Beijing
2017-09-27 19:32:59 cri
Hukumar zartaswa ta kasar Sin, ta gabatar wa mahukuntan birnin Beijing takardun bayanai, na adadin yawan al'umma da gine gine, wadanda aka tsara kasancewar su a birnin nan da shekarar 2020.

Bayanan dai sun nuna cewa bisa tsarin, mutane miliyan 23 ne za su kasance mazauna birnin nan da shekarar ta 2020, kuma ana fatan wannan adadi ya dore a shekaru masu zuwa.

Kaza lika takardun bayanan sun nuna cewa, an tsara rage filayen gine gine zuwa kimanin sakwaya kilomita 2,860 nan da shekara ta 2020, da kuma sakwaya kilomita 2,760 ya zuwa shekarar 2035.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China