Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson, zai kawo ziyara nan kasar Sin a ranar Asabar 30 ga watan nan na Satumba. Mr. Tillerson zai gudanar da ziyarar aikin ce bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi masa, kamar dai yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Lu Kang ya bayyana a yau Laraba.
Mr. Lu Kang ya ce jami'an biyu za su yi musayar ra'ayoyi da juna, game da batutuwan da suka shafi alakar kasashen su, da batun ziyarar aiki da ake sa ran shugaba Donald Trump zai gudanar nan gaba cikin wannan shekara a kasar Sin, da ma sauran batutuwan da suka shafi shiyya shiyya da ma na kasa da kasa.(Saminu Alhassan)