Sin: Ba za a iya daidaita batun nukiliya a zirin Koriya ta hanyar matakin soja ba
Game da halin da ake ciki a batun zirin Koriya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Talata cewa, yadda aka sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi, wani mataki ne na tunasar da kasar irin damuwar da gamayyar kasa da kasa ke nunawa, da nufin matsa mata komawa taburin shawarwari.
Har ila yau, a cewar jami'in, kasar Sin na fatan bangarorin Amurka da Koriya ta Arewa, za su lura da cewa, furta wasu kalamai na barazana, ba zai taimaka wajen warware batun nukiliya a zirin Koriya ba. Kana ta da wutar yaki zai haifar da illa ga kowa. (Bello Wang)