in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Somalia da AU na neman mafita game da barazanar ababen fashewa
2017-09-26 10:49:48 cri

Sojojin Somalia da na shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika AMISOM, sun kaddamar da wani taron yini 3 a jiya Litinin, domin nazarin barazanar dake tattare da ababen fashewa da tsara matakan rage su.

Taron wanda kuma ya samu halartar wakilai daga MDD da sojojin Birtaniya, ya tattauna kan karuwar barazana da hadduran ababen fashewa a kasar dake kahon Afrika.

Taron wanda shirin rage barazanar nakiyoyi da bama-bamai na MDD wato UNMAS ya dauki nauyin shiryawa, na da nufin samar da hanyoyin yaki da barnar ababen fashewa a Somalia.

Tattaunawar da za a yi, za ta mai da hankali kan takaita karuwar amfani da ababen fashewa da kungiyoyin 'yan ta'adda kamar Al-Shabaab ke yi.

Wakilin musammam na shugaban hukumar AU a Somalia Francisco Madeira, ya bukaci al'ummomin kasashen waje su shiga a dama da su, don ci gaba da mara baya ga shirin AMISOM, ta yadda zai samu damar rage hadduran da ababen fashewa ke da su a kan fararen hula da jami'an tsaro a Somalia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China