in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somalia ta haramtawa ministoci amfani da kafafen sada zumunta na zamani
2017-08-28 09:09:47 cri

Firaministan Somalia Hassan Khaire, ya umarci ministocin kasar su kauracewa amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yin tsokaci kan batutuwan siyasa masu muhimmanci.

Hassan Khaire ya kuma gargadi ministocin game da ganawa da kafafen yada labarai ba tare da neman izini daga ofishinsa ba.

Umarnin ya biyo bayan wasu bayanai mabambamtan da suka fito daga ministoci a ranar Juma'a da ta gabata, game da wani aikin soji da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 10.

Firaministan ya ce, ana sanar da dukkan ministocin da aka ba umarnin, su nemi izini daga ofishinsa, kafin amfani da kafafen sada zumunta na zamani da gidajen rediyo da talabijin da duk wani abu dake da alaka da yada labaran da ya shafi gwamnati.

Ya ce, daga yanzu, an haramta amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yin tsokaci game da muhimman batutuwan siyasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China