in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin jin kai a Somalia na kara tabarbarewa
2017-02-03 10:13:42 cri

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai jiya cewa, wani sabon gargadi na nuni da cewa, an samu tabarbarewar ayyukan jin kai a Somalia. Sannan, akwai alamomi masu tayar da hankali da ke nuni da cewa, akwai iyuwar samun fari a kasar cikin wannan shekarar.

Dujarric ya bayyana cewa, ofishin dake kula da ayyukan jin kai na majalisar ya ce, adadin mutanen dake bukatar taimako a kasar ya karu zuwa miliyan shida da dubu dari biyu, kusan rabin al'ummar kasar ke nan.

Ya ce, mutane kusan miliyan uku ne, ke fuskantar matsaloli da dama, ciki har da na rashin abinci.

Ya kara da cewa, har yanzu akwai yara dubu dari uku da sittin da uku, 'yan kasa da shekaru biyar, dake fama da tamowa, ciki har da dubu saba'in da daya dake cikin matsanancin hali, inda ya ce, halin da suke ciki ka iya kara ta'azzara, kuma ya kai su ga mutuwa.

Cikin wata sanarwa da jami'in MDD mai kula da ayyukan jin kai a Somalia Peter de Clercq ya fitar jiya Alhamis, ya yi gargadin cewa, muddin ba a dauki matakan gaggawa na ba da taimakon jin kai cikin makonni masu zuwa ba, nan ba da dadewa ba, za a fuskanci fari a wasu yankuna na kasar da suka yi fama da kamfar ruwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China