in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
kwamitin tsaron MDD ya sabunta kudurin yaki da 'yan fashin tekun Somaliya
2015-11-11 10:58:22 cri

A ranar Talatan nan kwamitin tsaron MDD ya sake sabunta kudurin shi ga hukumomin kasashe da yankuna na fada da 'yan fashin teku na wani karin shekara daya, yana mai lura da cewa, barazanar da ake ci gaba da fuskanta dalilin 'yan fashin teku da fashi da makami a kan ruwa tana kawo kalubale wajen isar da kayayyakin jin kai ga Somaliya, da ma yankin baki daya.

Kwamitin ya yi shawarar sabunta ikon da ya ba kasashe da yankuna waje hada kai da Somaliya a yakin da ake yi da 'yan fashin teku da fashi da makami a kan ruwa a gabar ruwan Somaliya na wani karin watanni 12, in ji sanarwar.

Ganin cewa ci gaba da samun rashin daidaito a Somaliya da ayyukan fashin teku da fashi da makami a kan ruwa a gabar ruwan kasar suna da alaka da juna, in ji kwamitin, yana mai jaddada cewa, akwai bukatar samar da damammakin tattalin arziki ga al'ummar kasar Somaliya.

Baya ga samar da kwarin gwiwwar ci gaba da hadin kai da mahukuntan Somaliya a yakin da take yi da 'yan fashin teku da fashi da makami a kan ruwan, kwamitin mai mambobi 15 ya kuma lura da cewa, muhimmin aikin mahukuntan Somaliya shi ne yaki da 'yan fashin teku da kuma fashi da makami a gabar ruwanta.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China