in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gina kamfanin hada magunguna a Habasha
2016-10-19 09:15:50 cri

A jiya Talata aka kaddamar da bikin ginin katafaren kamfanin harhada magunguna a garin Dukem, mai tazarar kilomita 40 daga Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Ana sa ran kamfanin wanda babban reshensa yake birnin Chongqing a kudu maso yammacin kasar Sin, zai zuba jari na kimanin dalar Amurka miliyan 85 wajen aikin ginin kamfanin harhada magunguna mai suna Sansheng.

Kamfanin zai samar da wuraren aikin yi sama da 300 ga 'yan asalin kasar.

Da yake jawabi a lokacin bikin kaddamar da aikin, ministan masana'antu na kasar Habasha Mebratu Meles ya ce, aikin ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatar sa, yayin da kasar ke kokarin daukar matakan yin garambawul ga sha'anin tattalin arzikinta. Meles ya yabawa aikin, ya ce, aikin zai kara habaka masana'antun magunguna dake kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China