in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kokarin yaki da cin hanci na Sin ya zama abin koyi ga Afrika
2016-01-19 10:41:46 cri

Matakin tsayawa tsayin daka na kasar Sin wajen bankado jami'ai da cin hanci yawa katutu ya zaman abin koyi ga nahiyar Afrika, inda wannan annoba take kara talautar da miliyoyin mutane, a cewar wani babban jami'in kasar Uganda.

Shirin shugaba Xi Jinping na farautar babu ja da baya jami'an da suke cin hanci shi ne matakin da miliyoyin masu faffutuka suke fatan gani a Afrika, kuma shugabannin Afrika za su iya daukar wannan misali.

Matakan da kasar Sin ta dauka sun kasance irin wadanda ake bukata wajen yaki da cin hanci a ko ina cikin duniya, in ji Simon Lokodo, ministan dake kula da yaki da cin hanci a cikin wannan kasa ta Uganda dake gabashin Afrika, a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua.

Ministan ya bayyana cewa, shirin kasar Sin dake zaman abin koyi, wata sabuwar nacewa wajen yaki da cin hanci a kasar Uganda, inda wannan annoba take barna.

Muna nuna yabo sosai da wannan aiki na kasar Sin. Za mu bi misalin kasar Sin ta hanyar daukar irin wadannan matakai domin kawar da karya lagon cin hanci, in ji mista Lokodo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China