in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samar wa Uganda taimakon abincin gaggawa
2017-03-01 10:30:15 cri

Jiya Talata aka kaddamar da bikin mika taimakon shinkafar da kasar Sin ta samar wa kasar Uganda a Kampala, fadar mulkin kasar, inda gwamnatin kasar Sin ta samar da taimakon shinkafa tan dubu 5 da dari 9 da tamanin da uku ga kasar ta Uganda domin sassauta matsalar karancin abincin da kasar ke fuskanta.

A jawabin da gabatar yayin bikin, firayin ministan Uganda Ruhakana Rugunda ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa tana kokarin sayen abinci domin warware matsalar, kana ya yabawa gwamnatin kasar Sin matuka da taimakon jin kai da ta samarwa kasarsa, ya ce, wannan wata alama ce ta sada zumunta dake tsakanin kasashen Sin da Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China