Ofishin jakadancin Sin dake kasar Zimbabwe ya dauki bakuncin gudanar da gasar a wannan karo. Jakadan Sin dake kasar Zimbabwe Huang Ping ya bayyana cewa, raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yana da nasaba da mu'amalar dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, ana fatan za a kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen biyu ta hanyar wasan.
A nasa bangare, ministan wasanni na kasar Zimbabwe Makhosini Hlongwane, ya nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga kasar Zimbabwe a fannonin wasan kwallon tebur, da iyo, da wasannin motsa jiki. Yana fatan jama'ar kasar Zimbabwe za su ji dadin wasan kwallon tebur kamar Sinawa. (Zainab)