in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Masar za su jagoranci wasu kasashen Afirka a gasar kwallon tebur da Jamus za ta karbi bakunci
2017-02-15 17:16:09 cri
Najeriya da Masar tare da wasu sauran kasashen Afirka 14, zasu shiga gasar kwallon tebur ta duniya wadda hukumar ITTF ke shiryawa, gasar da kuma za ta gudana nan gaba cikin wannan shekara a birnin Dusseldorf, na kasar Jamus.

'Yan wasan nahiyar Afirka wadanda suka yi fice a gasar bara, wadda aka buga a birnin Agadir na kasar Morocco ne za su wakilci nahiyar a Jamus ta Jamus.

Baya ga Najeriya da Masar, sauran kasashen daga Afirka sun hada da Algeria, da Botswana, da Kamaru, da Congo Brazzaville, da Cote d'Ivoire, da Gabon, da Libya, da Morocco. Sai kuma Afirka ta Kudu, da Senegal, da Saliyo, da Sudan, da Togo da kuma Tunisia.

Dan wasan Najeriya Aruna Quadri, da na Masar Omar Assar na cikin manyan 'yan wasa 100 mafiya kwarewa a wasan kwallon tebur, wanda hakan zai baiwa kasashen biyu damar shiga gasar da 'yan wasa hurhudu.

Daga nahiyar Turai kuwa 'yan wasa daga kasashe 45 ne za su halarci gasar, sai kuma Sin wadda ke rike da kambin gasar, wadda za ta jagoranci kasashe 37 daga nahiyar Asiya.

Sauran kasashen da suma za su shiga gasar da 'yan wasa hurhudu, sun hada da Belgium, da Croatia, da Czech, da Denmark, da England, da Finland, da Greece, da Hungary. Sai kuma India, da Iran, da Poland, da Qatar, da Romania, da Russia. Sauran sun hada da Singapore, da Slovenia, da Serbia, da Slovakia, da Sweden, da Turkiyya, da Ukraine da kuma Amurka.

A daya bangaren kuma kasashen da za su shiga gasar da 'yan wasa biyar-biyar sun hada da Austria, da Belarus, da Brazil, da Sin, da Faransa, da yankin Hong Kong, da kasar Japan, da koriya ta Kudu, da Portugal da yankin Taipei na Sin. Mai masaukin baki kuwa Jamus za ta gabatar da 'yan wasa 6 ne.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China